An tsare dan takarar Gwamnan Imo na APC
Jami’an tsaro sun kama dan takarar Gwamnan jihar Imo na jam’iyyar APC Sanata Hope Uzodinma don bincikensa akan karkatar da kudaden kwangila na hukummar tashar jiragen ruwa da ya kai kudi Dala miliyan 12. Shugaban kwamitin binciken dawo da kadarorin gwamnati na fadar shugaban kasa Cif Okoi Obono-Obla ya tabbatar wa majiyarmu ta hanyar sadarwan […]
Jami’an tsaro sun kama dan takarar Gwamnan jihar Imo na jam’iyyar APC Sanata Hope Uzodinma don bincikensa akan karkatar da kudaden kwangila na hukummar tashar jiragen ruwa da ya kai kudi Dala miliyan 12.
Shugaban kwamitin binciken dawo da kadarorin gwamnati na fadar shugaban kasa Cif Okoi Obono-Obla ya tabbatar wa majiyarmu ta hanyar sadarwan tarho. Inda ya ce an tsare Sanatan ne ranar Lahadi a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja.