An tsare hedimasta kan fyade ga ’yar shekara 4 a makaranta

’Yan sanda sun cika hannu da mai makarantar da ake zargi da yi wa daliba ’yar shekara hudu fyade

An tsare hedimasta kan fyade ga ’yar shekara 4 a makaranta

Kurkuku

Ma’aikatar ilimi ta rufe Makarantar Firameren Great Leaders International kan zargin mai makarantar da yi wa daliba mai shekaru hudu fyade.

Da take sanar da rufe makarantar da ke yankin Ime-Obi, Agbor a Karamar Hukumar Ika ta Kudu ta Jihar Delta, ma’aikatar ilimin jihar ta yi tir da danyen aikin a matsayin “rashin imani da tsabar kidahumanci.”

“’Yan sanda na tsare da wanda ake zarin, wato mai makarantar, domin ya girbi abin da ya shuka a matsayin izina ga masu irin halinsa,” in ji ma’aikatar.

Sanarwar da Babban Sakataren Ilimin ma’aikatar, Augustine Oghoro, ya fitar ta bayyana takaici bisa yadda malamin da aka ba wa kula da tarbiyya da ilimantar da kananan yara zai yi irin wannan aikin ashha.

Ya kara da cewa Great Leaders International na daga cikin haramtattun makarantun da ke jihar, kuma ma’aikatar ta dade da rufe ta.

Rundunar ’yan sandan jihar ta tabbatar da tsare wanda ake zargin tare da cewa tana gudanar da bincike kan lamarin.

Ma’aikatar ilimin ta gargadi iyaye kan cin mutuncin malamai saboda horas da ’ya’yansu.

Babban Sakatarenta, Augustine Oghoro, ya yi gargadin ne a yayin da yake batu kan yadda iyayen dalibai a wata makarantar sakandaren gwamnati suka kai wa malamin da ya ladabtar da dansu a hari, inda ta hakan suka yi ajalin malamin.

Irin haka ta kuma faru a watan Oktoba a Makarantar Sakandaren Ehwerhe da ke Agbarho, inda wani mahaifi ke jagorantar gungun wasu dalibai da ke hana malamai da sauran dalibai sakat.