An tsare jami’an Gwamnatin Borno da Boko Haram ta sako
Sojojin Najeriya sun tsare wasu jami’an Gwamnatin Jihar Borno guda biyar da kungiyar Boko Haram ta sako bayan ta yi garkuwa da su. Majiyarmu ta ce sojoji sun yi awon gaba jami’an da aka sako da wadanda suka shiga tsakani aka sako su zuwa barikin Maimalari da ke Maiduguri babban birnin jihar. Auren dan Atiku […]
Dakarun Soji
Sojojin Najeriya sun tsare wasu jami’an Gwamnatin Jihar Borno guda biyar da kungiyar Boko Haram ta sako bayan ta yi garkuwa da su.
Majiyarmu ta ce sojoji sun yi awon gaba jami’an da aka sako da wadanda suka shiga tsakani aka sako su zuwa barikin Maimalari da ke Maiduguri babban birnin jihar.
“Ina tabbatar maka da cewa an sako jami’an Ma’aikatar RRR (mai sake ginawa da tsugunar da jama’a a yankunan da aka tarwatsa) da aka yi garkuwa da su.
“Yanzu haka da muke magana suna hanyarsu ta dawowa Maiduguri”, inji majiyar.
Ta ce tun a makon jiya aka fara tattaunawa da kungiyar domin ganin ta sako jami’an da ta yi garkuwa da su.
Jihar Borno na daga cikin jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya da suka shafe shekara 10 suna fama da rikicin Boko Haram.
Ayyukan kungiyar wadda yanzu wani bangare nata ya yi mubaya’a ga kungiyar ISWAP ya yi sanadiyar gudun hijirar daruruwan dubban mutane, baya ga asarar rayuka da dukiyoyi a yankin Tabkin Chadi.