An tsare mahajjacin Najeriya saboda daukar abin tsintuwa a harami

Hukumomin Saudi Arebiya sun kama wani mahajjaci dan Najeriya bayan da suka hange shi ta na’urar sirri ya dauki wani abin tsintuwa a kasa a cikin masallacin haramin garin Makka. Jami’an tsaro sun kai mahajjacin wanda ba a bayyana sunansa ba zuwa wani wuri da ba bayyana ba. Da yake magana da gidan rediyon Amurka […]

An tsare mahajjacin Najeriya saboda daukar abin tsintuwa a harami

Hukumomin Saudi Arebiya sun kama wani mahajjaci dan Najeriya bayan da suka hange shi ta na’urar sirri ya dauki wani abin tsintuwa a kasa a cikin masallacin haramin garin Makka.
Jami’an tsaro sun kai mahajjacin wanda ba a bayyana sunansa ba zuwa wani wuri da ba bayyana ba.
Da yake magana da gidan rediyon Amurka a kan lamarin, Jakadan Najeriya a kasar Saudiyya, Alhaji Sani Yunusa, ya ce ba su kai ga gano inda aka kai  mahajjacin ba.
Alhaji Yunusa ya gargadi sauran mahajjata su guji daukar duk wani abu da ba nasu ba a harami.