An tsare mai kemis da ya yi wa yarinya fyaɗe, ta rasu a Kano

Ana zargin mai kemis ɗin da yi wa yarinyar fyaɗe lokacin da aka kai ta yin allura.

An tsare mai kemis da ya yi wa yarinya fyaɗe, ta rasu a Kano

Zama Kotu. (Hoto: Aminiya)

Kotun Majistare mai lamba 51 da ke zamanta a yankin Nomansland a Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Hajara Safiyyu Garba, ta aike da mai kemis ɗin da ake zargi da yi wa wata yarinya fyaɗe har ta rasu.

Mai gabatar da ƙara, Barista Zainab Aliko, ta shaida wa kotun cewa ana zargin mai kemis ɗin mai suna Manniru Ibrahim Fanisau, da laifin yi wa yarinya ‘yar shekara tara da haihuwa mai suna Rumaisa Sadiq, fyaɗe a yayin da aka kai ta wajensa don yi mata maganin zazzaɓin cizon sauro.

Lamarin ya yi sanadiyyar rasuwarta.

Sai dai wanda ake zargin, ya musanta laifin da ake zarginsa, wanda ya saɓawa sashe 283 da 221 na Kundin Pinal Kod.

Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 30 ga watan Satumba, 2024 don samun shawarar ma’aikatar shari’a duba da cewar kotun ba ta da hurumin sauraren ƙarar.

Haka kuma kotun ta bayar da umarnin tsare wanda ake zargin a gidan gyaran hali.

Aminiya ta ruwaito cewa tun da farko mahaifin marigayiyar, Malam Sadiq Muhammad ne, ya kai ta tare da ’yan uwanta biyu shagon mai kemis ɗin, inda ya kwantar da ita da nufin za a yi mata ƙarin ruwa.

Daga nan ya umarci mahaifin da ya mayar da sauran ’yan uwanta gida, wanda ta nan ya yi amfani da damar wajen yi mata fyaɗe.

Sai dai lokacin da mahaifin ya dawo sai ya iske tuni yarinyar ta rasu, wanda hakan ya sa ya ɗauke ta zuwa asibiti.

Likitoci sun gano cewar an yi wa yarinyar fyaɗe, wanda hakan ya yi sanadin rasuwarta.