An kai masu addinin gargajiya kurkuku kan hari a masallaci
Kotu ta sa a tsare su a kurkuku kan auka wa Musulmi suna sallah.
Wasu masu addinin gargajiya na tsare a gidan yari bayan sun kai wa Musulmi hari a masallaci.
Kotun Maistar da ke garin Ota a Karamar Hukumar a Ado Odo Ota ta Jihar Ogun ta tsare mutanen su biyar ne a ranar Alhamis kan harin da suka kai wa Musulmi a garin Idiroko da ke Jihar.
- Kotu ta yi watsi da bukatar Abduljabbar kan mukabala
- Cin makani kariya ce daga cutar suga da COVID-19 —RMRDC
Ta ba da marnin ne a lokacin da take sauraron shari’ar wata arangama tsakanin bagarorin biyu a lokacin bikin masu addinin gargajiya na Oro a garin Idirokoko da ke Karamar Hukuma Ipokia ta Jihar.
A lokacin bikin na Oro, masu addinin gargarjiya sun hana fita a yanin kin, wanda hakan ya gurgunta a harkoki.
Sanya dokar a ranar Asabar gabanin fara bikin nasu ya haifar da rudani da kuma ba wa hamata iska a ranar Talata inda masu addinin gargajiyar suka far wa Musulmi suna cikin sallah da yamma a masallaci.
Sun kuma sari wani limami mai suna Bola Wasiu da adda a kai, suka kuma farmaki sauran mutane da ke masallacin, ciki har da mata a lokacin.
Lamarin ya faru ne a Masallacin Umar Bin Kattab wanda shekaru biyu da suka wuce masu addinin gargajiyar suka kai hari a lokacin irin wannan biki nasu.
Amma a wannan karon, Musulmi sun yi wa uku daga cikin maharan kofar rago, sannan suka damka su a hannun ’yan sanda.
A ranar Alhamis ’yan sanda suka gurfanar da mutum biyar da ake zargi da hannun ahairn, a gaban kotun Mai Shari’a A O Adeyemi a Ota.
Kotun ta ba da belin masu addinin gargajiyar amma sun kasa cika sharudan da ta gindaya musu.
Don haka alkalin ya sa a ci gaba da tsare su a gidan yari zuwa ranar 24 ga watan Agusta, 2021, da za a ci gaba da sauraron kara.
Kakakin ’yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi ya ce an sha gayyatar masu addinin gargajiyar domin tattaunawar zaman lafiya.