An tsare masu fyade 140 a Katsina

’Yan sanda a Jihar Katsina sun cafke mutun 140 bisa zargin aikata fyade a fadin Jihar. Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Sunusi Buhu ya ce an damke mutanen ne bisa zargin aikata fyade sau 87 a watanni Afrilu zuwa Yuni a kananan hukumomin jihar guda 34. Ya ce dukkaninsu an gurfanar da su a gaban kotu […]

An tsare masu fyade 140 a Katsina

’Yan sanda a Jihar Katsina sun cafke mutun 140 bisa zargin aikata fyade a fadin Jihar.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Sunusi Buhu ya ce an damke mutanen ne bisa zargin aikata fyade sau 87 a watanni Afrilu zuwa Yuni a kananan hukumomin jihar guda 34.

Ya ce dukkaninsu an gurfanar da su a gaban kotu domin zama izina ga masu mummunar dabi’ar.

Sunusi Buba ya ce rundunar na aiki tare da shugabannin addini da sarakuna da iyaye da sauran masu ruwa da tsaki domin ganin bayan matsalar fyade a Jihar Katsina.

A don haka ya kuma roki ’yan jarida da kungiyoyin kare hakki su yi aiki tare da ’yan sanda wurin yakar matsalar fyade da cin zarafi.

Ya yaba da hadin kan da ke tsakanin hukumomin tsaro a jihar wajen yakar manyan laifuka.

Sannan ya yi kira ga jama’a da su taimaka wa jami’an tsaro da muhimman bayanai da za su kai ga dakile miyagun laifuka da samar da tsaron rayuka da dukiyoyi a jihar.