An tsare matasa uku kan zargin shirya hare-hare a Singapore

Mahukunta sun ce matasan, masu shekaru 14, 15 da 19, sun dilmiya cikin harkar tsattsauran ra’ayi ne da suka koya a intanet.

An tsare matasa uku kan zargin shirya hare-hare a Singapore

Mahukuntan ƙasar Singapore sun kama wasu matasa uku da ake zargin sun shirya kai hare-hare daban-daban da suka haɗa da daɓa wa mutane wuƙa, harbe-harbe da kuma tayar da bama-bamai.

Hukumar Tsaron Cikin Gida ta ƙasar (ISD) ta ce matasan, masu shekaru 14, 15 da 19, sun dilmiya cikin harkar tsattsauran ra’ayi ne da suka koya a intanet.

Ta ce daga cikin matasan waɗanda ake tsare su tun tsakanin watan Afrilu da Yuni, akwai wani saurayi mai shekara 14 da ya shirya kai hari da wuƙa a makarantar da yake karatu, inda ya yi niyyar kashe malamai da ɗaliban da ba Musulmi ba tare da yaɗa harin kai tsaye a intanet.

Haka kuma, akwai wani ɗan shekara 19 da ake zarginsa da shirya kai hari da wuƙa kan sojoji da wasu ɗalibai, yayin da ɗan shekara 15 yake matakin farko na shirin tayar da bam.

Hukumar ta ce duk cikin matasan uku babu wanda ya haɗa baki da wani, amma dukkansu sun ɗauki tsattsauran ra’ayi ne ta hanyar intanet, lamarin da ta ce na nuna barazanar da tsattsauran ra’ayin matasa ke ƙara haifarwa a ƙasar.