An tsare matashi kan ce wa budurwa ‘kin iya Kunu’ a Kano
Matashin ya fusata budurwar har ta shigar da kara a kan damun ta da maganar ‘kunu’.
’Yan sanda a Kano sun tsare wani matashi a bayan kanta saboda ya tsokani wata budurwa da salon ‘kin iya kunu’.
Kakakin ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce matashin ya dinga bin budurwar ce yana tsokanar ta cewar ta iya yin kunu.
- Me Ya Sa Ake Daukar Masu Kwarewar Aiki Fiye Da Masu Digiri?
- Musulma ta raba wa marayu da zawarawa Kirista kayan Kirsimeti a Kaduna
Kiyawa, ya wanda ya sanar da hakan shafinsa na Facebook ya kara da cewa, “Yanzu haka wannan matashin yana tsare a bayan kanta.”
Jami’in wanda ya ce “Baki shi kan yanka wuya.!” ya bayyana cewa matashin ya ga wata baiwar Allah tana tafiya a gefen titi, ya bi ta yana ta ce mata, “Kin iya Kunu?”.
“Har ya fusata ta, ta je ta shigar da korafi a ofishin ’yan sanda; Yanzu haka wannan matashin yana tsare a bayan kanta.
“Gani ga wane…,” kamar yadda ya wallafa.
A kwanakin baya ne dai sarar tambayar budruwa ko ta iya kunu ya bulla a shafukan sada zumunta a tsakanin matasa.
Samari sun dinga bidiyon jaddada muhimmancin kunu a gare su, suna zolayar ’yan mata a kan ko sun iya yin kunun ko akasin haka.
A wani salo na tata bera bari, har bidiyon barkwanci na zuwa neman aure a fasa saboda rashin iya kuna aka yi ta yi.
An dai jima ana kai ruwa rana kan batun na iya yin kunu, har ta kai ga matan sun fara yin bidiyon raddi.