An tsare matashi saboda dukan mahaifiyarsa

Kotun Shari’ar Musulunci da ke Sabon Gari a birnin Kano ta tsare wani matashi bisa zarginsa da laifin dukan mahaifiyarsa. dan sanda mai gabatar da kara Sufeto Ahmad Musa ya bayyana wa kotun cewa kanen wanda ake zargin ne ya kai musu kara cewa yayansa mai suna Abdulmuminu Muhammad ya zame musu alakakai a gidansu, […]

An tsare matashi saboda dukan mahaifiyarsa
An tsare matashi saboda dukan mahaifiyarsa

Kotun Shari’ar Musulunci da ke Sabon Gari a birnin Kano ta tsare wani matashi bisa zarginsa da laifin dukan mahaifiyarsa. dan sanda mai gabatar da kara Sufeto Ahmad Musa ya bayyana wa kotun cewa kanen wanda ake zargin ne ya kai musu kara cewa yayansa mai suna Abdulmuminu Muhammad ya zame musu alakakai a gidansu, sakamkon dukan mahaifiyarsu da yake yi a duk lokacin da ta yi masa fada idan ya yi wani laifi.
Mahaifiyar wanda ake zargin ta nemi kotu ta raba ta da danta gaba daya, domin a cewarta ba ta san abin da zai yi mata nan gaba ba.”Ina rokon alkali ya raba ni da shi, domin ban san abin da zai yi min nan gaba ba. Wallahi na hakura da shi,” inji mahaifiyar.  
Wanda ake zargin ya amsa laifinsa inda ya dora alhakin haka a kan shaye-shayen miyagun kwayoyi da yake yi, sannan ya nemi kotun ta yi masa afuwa.
 Alkalin Kotun Mai shari’a Abubakar Mahmud Ayagi ya bayar da umarnin a tsare matashin a gidan maza tare da dage shari’ar zuwa ranar 14 ga Agustan nan.   
A wani labarin an tsinci gawar wani matashi dan Unguwar Hausawa a yankin Tarauni, Kano kwance cikin jini a cikin filin Social Welfare da ke Gyadi-Gyadi.
Binciken Aminiya ya gano cewa akwai rashin jituwa tsakanin marigayin mai suna Nafi’u Abdullahi mai shekara 19 da wani matashi mai suna Nura Adamu Garko wanda dan unguwarsu ne kuma ake zargi da kashe marigayin.
An ce ranar da lamarin ya auku marigayin ya je gidan abokin rigimar tasa inda ya yanke shi da wuka, lamarin da ya jawo wanda ake zargin da kanensa Abdulalhi Adamu Garko suka biyo marigayin zuwa filin Social Welfare don daukar fansa.
Majiyar Aminiya ta ce ba a jima da shigar matasan cikin filin ba sai labarin tsintar gawar marigayin ya watsu inda jama’a ke zargin cewa matashin da kanensa ne suka kashe marigayin.
Wani dan unguwar ya shaida wa Aminiya cewa lokacin da jama’ar unguwar suka ga gawar Nafi’u sun dauke ta zuwa Asibitin Nasarawa inda aka tabbatar da rasuwarsa.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ASP Magaji Musa Majiya ya tabbatar wa Aminiya da faruwar lamarin inda ya ce wanda ake zargin ya gudu sai dai sun kama kanensa da ake zargin da shi suka hallaka marigayin. “Lokacin da muka gano wanda ake zargin na farko wato Nura Adamu Garko ya gudu, sai muka kama kanensa Abdullahi Adamu Garko saboda shi ma ana zargin da hanunnsa a kisan marigayin. Muna ci gaba da fadada bincike don gano gaskiyar lamarin. Idan mun same su da laifi za mu gurfanar da su gaban kotu,” inji Majiya.