An tsare mawakin Najeriya da ya yi wakar ‘Buga’ a Tanzaniya
Za a gurfanar da shi a kotu bisa dokokin kasar
’Yan sandan kasar Tanzaniya sun cafke mawakin Najeriyar nan da ya yi wakar nan da take tashe a sassa daban-daban na duniya mai taken Buga, wato Kizz Daniel.
Rahotanni sun ce an kama shi ne saboda ya ki zuwa wajen wani shagali da aka tsara zai rera wakar tasa mai farin jini.
- Gwamnati da ’yan adawar Chadi sun yi sulhu a Qatar
- Muzaharar Ashura: An kashe mana mutum 6 a Zariya — ’Yan Shi’a
An ce an ga lokacin da ’yan sanda suka cik hannu da shi kuma suka jefa shi a motarsu a babban birnin kasar na Dar-es-Salaam.
Bayanai sun ce an kama Kizz Daniel, wanda asalin sunansa shi ne Oluwatobiloba Daniel Anidugbe, ne saboda saba alkawari, kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu bisa dokokin kasar.
A wani bidiyo na daban da ya karade gari kuma, an ga wasu dandazon masoya da suka biya kudi domin kallon wasan amma burinsu bai cika ba, suna hargitsa filin wasan.