An tsare mutane 300 a gidajen yarin Kano ba bisa ka’ida ba —’Yan Sanda

Wasunsu sun shafe shekaru a tsare, amma babu shaidar an taba kai su kotu

An tsare mutane 300 a gidajen yarin Kano ba bisa ka’ida ba —’Yan Sanda

Wasu fursunoni a gidan yari

An gano mutane 300 da ke tsare a gidajen yari ba tare da shaidar sun aikata laifi ba a Jihar Kano.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa wasu daga cikin tsararrun sun shafe shekaru a gidajen yari, amma babu shaidar da ke nuna an taba kai su kotu ko lafin da ake zargin su.

Kwamitin lauyoyin da Shugaban yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya kafa ne ya gano tsararru 300 a gidajen yarin Kano, wadanda babu bayanan laifukan da ake zargin su da aikatawa.

Kwamitin lauyoyin ya gano haka ne a lokacin ziyarar ba-zata da ya kai wa gidajen yarin da ke Jihar Kano ranar Laraba.

Kwamitin, karkashin jagorancin kwamishinan ’yan sandan jihar Kano, Muhammad-Hussaini Gumel, na da alhakin bincike kan tauye hakkin tsararru a gidajen yari.

Gumel ya bayyana cewa aikin kwamitin ya kunshi ganowa da daukar bayanan tauye hakki a gidajen yari da kuma mika su ga hukumomin da ya dace domin daukar mataki.

Da yake gabatar da wasu tsararru a Gidan Gyaran Hali na Kurmawa, wani jami’in wajen, ya shaida wa kwamitin cewa akasarinsu, tun kafin a kawo su babu kundin abin da ake zargin sun aikata.

Wasunsu kuma, babu takaimaimen kotun da za a kai su, wasu babu shaidar an kai su kotu, amma duk da haka sun shafe shekaru a tsare a gidan yarin.

Daga cikinsu kuma akwai wadanda suke tsare saboda rashin kudin daukar lauyan da zai kare su.

Cikin tsararrun, akwai wani wanda ya ce tun shekarar 2009 aka tsare shi kan zargin kisa, amma har yanzu ba a taba kai shi kotu ba.

Akwai kuma wani wanda ya ce rabon da a kai shi kotun tun shekarar 2017, kuma har yanzu bai san makomarsa ba.

Amma a karshe, kwamitin ya ba wa tsararrun tabbacin samun adalci nan gaba kadan.