An tsare shi don ya kira lambar jami’an tsaro sau 5,000

’Yan sanda sun tsare wani mutum a kasar Japan bayan da ya kira lambar jami’ar tsaro saboda motar daukar marasa lafiya ta sha gaban motar shi akan titin, kamar yadda kafar yada labarai ta Odd News Blog ta bayyana.  Rundunar ’yan sandan kasar ta ce ta tsare mutumin ne mai suna, Atsuhiko Fuse, mai kimanin […]

An tsare shi don ya kira lambar jami’an tsaro sau 5,000
An tsare shi don ya kira lambar jami’an tsaro sau 5,000

’Yan sanda sun tsare wani mutum a kasar Japan bayan da ya kira lambar jami’ar tsaro saboda motar daukar marasa lafiya ta sha gaban motar shi akan titin, kamar yadda kafar yada labarai ta Odd News Blog ta bayyana. 

Rundunar ’yan sandan kasar ta ce ta tsare mutumin ne mai suna, Atsuhiko Fuse, mai kimanin shekara 52 bayan ya kira lambar neman agajin gaggawa ta 199 har sau dubu biyar ba tare da cewa komai ba. Kuma sun ce ya yi kiraye-karayen wayar ne tsakanin ranar 6 ga watan Fabrairun zuwa ranar 30 ga watan Maris. Ana dai tuhumarsa ne da laifin neman kawo cikas.
Kodayeke, lokacin da ake masa tambayoyi Mista Atsuhiko ya shaida wa ’yan sanda cewa ya fusata bayan da motar daukar marasa lafiya ta sha gabansa lokacin ya tuki.