An tsare shi kan zargin yin luwaɗi da ’ya’yan maƙwabcinsa 5 a Zariya

Yaran sun tabbatar da cewar wanda ake zargin ya yaudare su ta hanyar ba su alawa.

An tsare shi kan zargin yin luwaɗi da ’ya’yan maƙwabcinsa 5 a Zariya

Zama Kotu. (Hoto: Aminiya)

An tsare wani mutum, mai suna Alkasim Lashe Moni a gidan gyaran hali kan zargin sa da yin luwaɗi da yaran maƙocinsa biyar a Ƙaramar Hukumar Makarfi a Jihar Kaduna.

Wani lauya mai zaman kansa da ke Zariya, Ibrahim B. Ahmed, ya buƙaci Gwamnatin Kaduna da masu ruwa da tsaki su ɗauki matakin kare cin zarafin ƙananan yara da ya zamo ruwan dare a tsakanin al’umma.

Barista Ahmed, ya yi wannan kiran ne, yayin da yake bayyana jimaminsa kan mutumin da ake zargi mai sana’ar sayar da hatsi, mazaunin Layin Rimi a garin Makarfi ya lalata ‘ya’yan maƙocinsa guda biyar.

Lauyan ya bayyana lamarin a matsayin abun tashin hankali saboda yadda matsalar ke neman zama barazana a cikin al’umma.

Da yake bayanin yadda lamarin ya faru, mahaifin yaran, Nura M. Yusha’u, ya ce wanda ake zargin ya yaudari yaran sannan ya lalata su.

Ya ƙara da cewa a halin da yaran ke ciki yaran ba sa iya rike bayan gida, saboda lalata masu dubura da mutumin ya yi, kuma babu wani magani da aka yi musu saboda rashin kuɗi.

Har ila yau, ya bayyana cewa har ma kuɗi wasu masu rajin kare haƙƙin ɗan Adam suke nema a wajensa da sunan taimako

Ya koka kan cewar ba shi da kuɗi, wanda hakan ne ya sa yake neman lauyan da zai tsaya masa.

Aminiya ta ji ta bakin yaran, inda suka tabbatar da faruwar lamarin, amma sun ce mutumin yana yaudarar su ne.

Wanda ake zargin yana tsare a gidan gyara hali a Kaduna, bayan da ‘yan sanda suka gurfanar da shi a kotu.

A gefe guda kuma ana raɗe-raɗin cewar an sanya gidan wanda ake zargi a kasuwa domin samun kuɗin da za a kashe maganar.

Mahaifiyar Gwamnan Jigawa ta rasu

Najeriya ba ta cikin ƙasashen da suka fi cin bashi a Afirka – IMF

Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Babiana

An horar da mutum 500 dabarun adana ruwa don inganta muhalli a Gombe