An tsare shugabar kasa saboda mallakar rediyo

Ana zargin Shugaban Kasar da sayen rediyo daga kasar waje ba da izini ba.

An tsare shugabar kasa saboda mallakar rediyo

Aung San Suu Kyi

Jami’an tsaro sun tsare Shugabar Kasar Myanmar, Aung San Suu Kyi saboda mallakar rediyon sadarwa guda hudu ba bisa ka’ida ba.

Shugaan kasar za ta ci gaba da zama na kwana 11 a tsare a hannun ’yan sanda zuwa ranar 15 ga watan Fabrairu, saboda zargin karya dokokin kasar na shigo da kaya daga kasashen waje.

An gano rediyoyin ne a samamen da aka kai gidan Shugabar Kasar da sojoji suka yi wa juyin mulki a birnin Naypyidaw, inda a yanzu ake tsare da ita, take kuma fuskantar zargin amfani da rediyoyin ba bisa ka’ida ba.

Takardar tuhumar ta ce baya ga shigo da su ba bisa ka’ida ba, kuma ba a yi musu rajista ba, Shugabar Kasar mai shekara 75 ta ba wa dogarawanta su suna amfani da su ba dsa izini ba.

A cewar takardar, ana tsare da Aung San Suu Kyi ne “domin a yi wa shaidu tambayoyi, a karbi hujjoji sannan a ji ta bakin lauyoyi bayan ita ma an yi mata tambayoyi.”

’Yan sanda na kuma tuhumar tsohon Shugaba Win Myint da aka hambarar da mulkinsa a wata shari’a da ake tuhumar sa karkashin dokar kasar ta Kare Aukuwar Ibtila’i.

Borin kunyar sojoji

Daraktan Burma Campaign UK, Mark Farmaner ya ce zargin da ake wa Mis Suu Kiyi alama ce da ke nuna har yanzu sojojin na cike da tsoro.

“Gaskiyar maganar ita za su daure ta ne saboda har yanzu suna tsoron ta,” inji shi.

Sojojin Myanmar sun dage a kan cewa sun hambarar da gwamnatin Mis Suu Kyi ne saboda tarzomar da ta biyo bayan ‘magudin zaben’ watan Nuwamba, duk kuwa da kiraye-kirayen da ake ta yi a kasar cewa su karbi sakamakon zaben.

Kungiyar ’Yan Majalisa Masu Kare Hakkin Dan Adam na Yankin Kudu maso Gabashin Asiya sun ce juyin mulkin na zai “fama gyambo” ga miliyoyin ’yan kasar da suka kada kuri’a a zaben, kuma hakan na iya mayar da kasar cikin bakin mulkin soji na kama karya.

“Zarge-zargen abin dariya ne,” inji Shugaban Kungiyar Charles Santiago.

“Wanna abun da sojojin suka yi sun yi ne don su halasta juyin mulkin da suka yi wa halastacciyar gwamnatin da aka zaba a kasar Myanmar.”

Likitoci na yajin aiki

Ma’aikatan lafiya a asibitoci 70 da hukumomin lafiya a garuruwa 30 a fadin kasar sun fara yajin aikin nuna adawarsu ga juyin mulkin.

Suna zargin sojojin da fifita son zuciyarsu a kan rayuwar mutane a lokacin annobar coronavirus da ta yi ajalin mutum 3,100 a kasar.

“Ba za mu bi duk wani umarni daga haramtacciyar gwamnatin sojojin da suka nuna ba su damu da damuwar talakawa marasa lafiya ba,” inji su.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya