An tsare tsohon Shugaban KASCO a gidan yari kan N3.2bn

Kotu ta tsare tsohon Manajan-Daraktan Hukumar Kayayyakin Noma ta Jihar Kano (KASCO), Bala Muhammad Inuwa kan zargin satar Naira biliyan 3.2

An tsare tsohon Shugaban KASCO a gidan yari kan N3.2bn

(Hoto: us.fotolia.com)

Babbar Kotun Jihar Kano ta tsare tsohon Manajan-Daraktan Hukumar Kayayyakin Noma ta jihar (KASCO), Bala Muhammad Inuwa kan zargin satar Naira biliyan 3.2 daga asusun gwamnatin jihar.

Kotun ta ba da umarnin tsare shi ne a yayin ci gaba da sauraron shari’ar da ake zargin shi da dansa aikata laifuka 10 da suka danganci raba wa mukarrabansu Naira biliyan 3.2.

Lauyan gwamnatin jihar, Zaharadeen Hamisu Kofar Mata, ya ce masu gabatar da kara sun mika wa kotun gamsassun hujjoji da shaidun da ya kamata, domin ta hukunta wadanda aka zargin.

Ya kuma kalubalanci bukatar lauyan wadanda ake kara, Farfesa Nasiru Adamu Aliyu, na nema beli.

Sai dai a martaninsa, Farfesa Nasiru ya ce, lauyan masu kara da neman a hukunta wadanda ake zargi ba tare an bi tsarin da ya dace ba, don haka ya bukaci kotu kada ta biye wa bangaren masu kara.

Bayan sauraron bangarorin ne alkalin kotun, Mai Shari’a Hafsat Sani Yahya ta bayyana cewa masu kara sun gabatar da wadatattun shaidu da hujjoji da za a iya ci gaba da shari’ar.

Don haka ta bukaci lauyan wanda ake kara ya kara shigar da bukatar neman beli, wanda ta ce za ta karba.

Daga nan ta dage zaman zuwa ranar 6 ga watan Disamba, 2023.

 

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan