An tsare wadanda ake zarginsu da yin garkuwa

Kotun majistare a jihar Kano ta tsare mutane uku a gidan yari bisa zargin yin garkuwa da wani dan kasuwa Usman Abdullahi. Mutanen da aka tsare wadanda ake zarginsu da yin gakuwan sun hada da: Abubakar Abdullahi wanda aka fi sani da Daffi da Hashim Mustapha da kuma Anthony Nwike wanda kotun ta gurfanar da […]

An tsare wadanda ake zarginsu da yin garkuwa

Kotun majistare a jihar Kano ta tsare mutane uku a gidan yari bisa zargin yin garkuwa da wani dan kasuwa Usman Abdullahi.

Mutanen da aka tsare wadanda ake zarginsu da yin gakuwan sun hada da: Abubakar Abdullahi wanda aka fi sani da Daffi da Hashim Mustapha da kuma Anthony Nwike wanda kotun ta gurfanar da su a gaban babbar mai yanke hukunci ta kotun Majistirin, Aisha Mohammed Yahaya.

Da farkon samun rahoton dai an bayyana cewa wasu ne da ba a san ko suwa ye ba suka yi garkuwa da Abdullahi a ranar 15 ga watan Agusta 2018.

‘Yan sanda ne dai suka kama wadanda ake zargin.