An tsare wanda ake zargi da sace yaro da yin luwadi da shi
Wani maigadi a unguwar Shaho a garin Karmo da ke yankin Birnin Tarayya Abuja, mai suna Usman Idris ya gurfana a gaban Kotun Lardi ta Birnin Tarayya da ke Jiwa bisa zarginsa da sace wani yaro mai shekara tara inda ake zarginsa da yi masa fyade. dan sanda mai gabatar da kara a kotun, Sani […]
Wani maigadi a unguwar Shaho a garin Karmo da ke yankin Birnin Tarayya Abuja, mai suna Usman Idris ya gurfana a gaban Kotun Lardi ta Birnin Tarayya da ke Jiwa bisa zarginsa da sace wani yaro mai shekara tara inda ake zarginsa da yi masa fyade.
dan sanda mai gabatar da kara a kotun, Sani Idris na babban ofishin ’yan sanda na Karmo, Abuja ya shaida wa kotun cewa, wanda ake zargin Usman Idris mai shekara 46, mahaifiyarsa ce ta gabatar da karar a ofishinsu, ta kuma ce wanda ake zargin ya dauki yaron ne bayan ta aike shi ya debo mata ruwa a unguwarsu,
Ta ce daga nan ne ya killace shi a wani daki a gidan da yake aiki na tsawon wata daya da mako biyu, yana aikata luwadi da shi a tsawon wannan lokaci kafin ya samu kubucewa. A cewar mai shigar da karar wanda ake zargin ya amince da aikata al’amarin a lokacin da ake yi masa bincike.
Da alkalin kotun Muhammad Lawal Munnir ya waiwayi wanda ake zargin ya musanta aikata lamarin.
Daga nan ne kotun ta ba da umarnin tsare shi a kurkuku har zuwa ranar 21 ga watan Afirilu lokacin da za a ci gaba da sauraron karar