An tsare wanda ya sa wa karensa ‘Buhari’ a Kurkuku

A jiya Talata ne wata kotun majistire da ke a Sango Ota a Jihar Ogun ta umarci a ci gaba da tsare Joe Chinakwe, mutumin nan da ya sanyawa karensa suna Buhari. Rundunar ‘yan sandan jihar ce dai ta gurfanar da Joe Fortomose Chinakwe a gaban kotun majistare, bisa zargin shirin ta da zaune tsaye, […]

An tsare wanda ya sa wa karensa ‘Buhari’ a Kurkuku
An tsare wanda ya sa wa karensa ‘Buhari’ a Kurkuku

Mista Joe Fortomose ChinakweA jiya Talata ne wata kotun majistire da ke a Sango Ota a Jihar Ogun ta umarci a ci gaba da tsare Joe Chinakwe, mutumin nan da ya sanyawa karensa suna Buhari.

Rundunar ‘yan sandan jihar ce dai ta gurfanar da Joe Fortomose Chinakwe a gaban kotun majistare, bisa zargin shirin ta da zaune tsaye, sakamakon yawon da yake yi da karensa, wanda ya rubuta sunan Buhari a sassan jikin karen.

Kotun dai ta ba da belinsa, to sai dai bai cika sharudan beli ba, don haka aka ci gaba da tsare shi a gidan kason Ibara Prison, kamar yadda BBC ta bayyana.

Tun da farko dai shugannin kananan kabilun dake zaune a jihar ta Ogun sun shiga tsakani da niyyar kawo karshen tuhumar da ake yiwa mutumin.

To sai dai rundunar ‘yan sandan jihar ta sake gayyatar sa inda ta gurfanar da shi a kotu.

Sarkin Hausawan jihar ya ce za su sake wani yunkurin na karbar belin Joe Fortomose Chinakwe da kuma nufin janye tuhumar da ake yi masa, a wani mataki na sasanta batun.

Ranar 19 ga watan gobe ne dai za a ci gaba da shari’ar.