An tsare wanda ya yi wa mahaifinsa fashi
Wata kotun Majistare da ke Zungeru a birnin Kano ta bayar da umarnin a tsare wani matashi mai kimanin shekara 25 bisa zarginsa da laifin yi wa mahaifinsa fashi da bindiga. Ana zargin matashin mai suna Musa Isa da ke zaune a kauyen Motar Kara ne a karamar Hukumar Doguwa ta Jihar Kano, inda ya […]
Wata kotun Majistare da ke Zungeru a birnin Kano ta bayar da umarnin a tsare wani matashi mai kimanin shekara 25 bisa zarginsa da laifin yi wa mahaifinsa fashi da bindiga.
Ana zargin matashin mai suna Musa Isa da ke zaune a kauyen Motar Kara ne a karamar Hukumar Doguwa ta Jihar Kano, inda ya hada kai da wasu mutum bakwai da suka tsere suka yi wa mahaifinsa dukan kawo wuka tare da dauke masa babur.
An shaida wa kotun cewa wanda ake zargin da abokansa sun dauki makamai da suka hada da bindiga da gatari suka auka wa gidan mahaifinsa suka rika harbi a iska sannan suka dauke babur dinsa da kimar kudinsa ya kai Naira dubu 130, daga bisani suka yi masa dukan kawo wuka ta amfani da sanduna har ya samu karaya a kafarsa ta dama.
Kotu ta samu matashin da laifuffukan hadin baki da fashi da makamni da jin rauni, wadanda laifuka ne da suka saba wa sashi na 1(a) da (b) na kundin manyan laifuffuka.
Yayin da aka waiwayi matashin ya musanta laifin da ake zarginsa da shi, ya ce duk da dai ya san shi barawo ne tare da sauran abokansa da ake zarginsu, amma ba ya cikin mutanen da suka far wa mahaifinsa.
Alkalin kotun Mai shari’a Fauziyya Isa Sheshe ta dage sauraren shari’ar zuwa ranar 27 ga Mayu don duba ko kotun tana da hurumin sauraron karar.