An tsare wata mata kan zargin kashe ’yarta da maganin ɓera a Kaduna
Alƙalin kotun, Samson Kwasu, ya ce kotun ba ta da hurumin sauraron shari’ar.
Wata Kotun Majistare da ke Kafanchan, a Jihar Kaduna, ta bayar da umarnin tsare wata mata mai suna Mercy Michael, mai shekaru 30, a gidan gyaran hali kan zargin kashe ’yarta, ’yar wata takwas ta hanyar ba ta maganin ɓera.
Hukumar tsaro ta Sibil Difens ce, ta gurfanar da ita a gaban kotu kan zargin aikata kisan kai.
Laifin da ya saɓa wa Sashe na 189 na Dokar Laifuffuka ta Jihar Kaduna.
Mai gabatar da ƙara, Marcus Audu, ya shaida wa kotun cewa wani mai suna Godfrey Sunday daga unguwar Fadia Bakut, Zonkwa ne, ya kai rahoton faruwar lamarin ofishin NSCDC a ranar 11 ga watan Disamba.
A cewarsa, a ranar 10 ga watan Disamba, Mercy ta bai wa jaririyar maganin ɓera.
Ya ce an garzaya da jaririyar zuwa Babban Asibitin Zonkwa, amma washegari ta rasu.
Bayan haka, an kai rahoton lamarin cibiyar Salama Sexual Assault Referral Center da ke Kafanchan kafin aka miƙa batun ga NSCDC domin ci gaba da bincike.
Mai gabatar da ƙara ya bayyana cewa wacce ake zargi ta amsa laifin a lokacin bincike.
Alƙalin kotun, Samson Kwasu, ya ce kotun ba ta da hurumin sauraron shari’ar.
Saboda haka, ya umarci masu gabatar da ƙara su miƙa takardun shari’ar ga Daraktan Gurfanarwa na Jihar Kaduna don neman shawara.
An ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 17 ga watan Disamba.