An tsare yaron alkali kan yi wa budurwa ciki
Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci da ke karamar Hukumar Garki a Jihar Jigawa a karkashin jagorancin Mai shari’a Aliyu Haruna Roni ta tsare waadansu matasa ciki har da wani yaron alkali a gidan maza saboda zarginsu da laifin yi wa wata budurwa ciki.Wadanda aka aike gidan mazan sun hada da Aliyu Nasiru da Bello Garba […]
Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci da ke karamar Hukumar Garki a Jihar Jigawa a karkashin jagorancin Mai shari’a Aliyu Haruna Roni ta tsare waadansu matasa ciki har da wani yaron alkali a gidan maza saboda zarginsu da laifin yi wa wata budurwa ciki.
Wadanda aka aike gidan mazan sun hada da Aliyu Nasiru da Bello Garba Liman, kuma Aliyu Nasiru an ce shi ne yaron alkalin da yake lura da masaukinsa, inda ake zargin ya yaudari yarinyar ya ce zai sama mata aikin allurar rigakafin Poliyo inda yake kai ta masaukin alkalin yana yin lalata da ita.
Wata majiya mai tushe ta shaida wa wakilinmu cewa iyayen budurwar da shi saurayin sun hada baki su zubar da cikin da majiyar ta ce ya kai wata biyu tare da ita.
Shi kuma Bello Liman an ce ya yi mata karya ne cewa zai aure ta, inda ta haka ne ya samu damar yin lalata da ita.
Yarinyar wadda aka sakaya sunanta ta shaida wa ’yan Hisba cewa kotu ta tura ta zuwa asibitin Gumel domin tabbatar da faruwar lamarin wato bincike a kan cikin da aka zubar.