An tsige DPO kan tsare lauya
An sauke wani DPO na Caji Ofis din Gowon Estate, saboda tsare wani lauya ba bisa ka’ida ba.
An sauke wani DPO daga kujerarsa saboda tsare wani lauya ba bisa ka’ida ba.
A ranar 30 ga watan Disamba, 2023 ne DPO din da aka cire ya ba da umarnin tsare Barista Olumide Sonupe, a lokacin da lauyan ya je ofishin domin karbar belin wanda yake karewa.
Bayan sakin lauyan mai shekau 36, sai da aka kwantar da shi a asibiti saboda kawamu da rashin lafiya.
- An kashe mai unguwa an yi wa mai gadi yankan rago a Katsina
- NAJERIYA A YAU: Anya Tinubu Na Duba Makomar Siyasarsa?
Kakakin ’yan sandan Legas, Benjamin Hundeyin, ya ce, kwamishinan ’yan sandan jihar ya ba da umarnin gudanar da bincike kan DPOn da aka sauke, wanda tuni jama’a ke ce-ce-ku-ce kan abin da ya yi wa lauyan.
Hundeyin ya ce, an cire DPO din ne bayan kammala bincike, kuma “CP Fayoade ya umarci jami’i mai kula da harkokkin shari’a ya tuntubi Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) Reshen Jihar Legas domin tattaunawa da nufin hana aukuwar irin haka a nan gaba.”