An tsige mataimakiyar shugaban Philippines Sara Duterte
Sara Duterte ’yar tsohon shugaban ƙasar Philippines, Rodrigo Duterte ce, wanda shi ma ke fuskantar zargin kashe dubban mutane.
FILE PHOTO: Philippine Vice President Sara Duterte delivers a statement following her impeachment by the lower house of the Congress, in her office at Mandaluyong City, Metro Manila, Philippines, February 7, 2025. REUTERS/Eloisa Lopez/File Photo
Majalisar Wakilan ƙasar Philippines ta tsige mataimakiyar shugaban ƙasar, Sara Duterte, a ranar Litinin bayan samunta da laifin tara dukiyar da ba a san tushenta ba, da kuma zargin yi wa Shugaban Ƙasa Ferdinand Marcos Jr barazanar kisa.
Kudurin tsige ta ya samu goyon bayan ’yan majalisa 257, yayin da 25 suka maƙale a kujerar naƙi, sai kuma tara da ba su halarci zaman ba.
- Sojoji sun yi kuskuren kashe fararen hula 13 a Neja
- Sahun farko na maniyyatan Sakkwato sun sauka a Madina
Bayan wannan mataki, ana sa ran za a miƙa batun gaban Majalisar Dattawa domin ci gaba da shari’a kan zarge-zargen biyu, waɗanda ake ganin na iya zama babbar barazana ga burinta na tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2028.
Sara Duterte ’ya ce ga tsohon shugaban ƙasar Philippines, Rodrigo Duterte, wanda shi ma ke fuskantar zarge-zargen hannu a kashe dubban mutane a lokacin da yake magajin garin Davao da kuma lokacin da yake shugaban ƙasar.
Haka kuma, tsohon shugaban rundunar ’yan sandan ƙasar, Roland dela Rosa, na fuskantar irin wannan tuhuma ta kashe dubban fararen hula a lokacin mulkin Rodrigo Duterte.