An tsige Shugaban Majalisar Dokokin Kebbi

’Yan Majalisar sun tsige shugabansu da Mataikaminsa a safiyar Talata.

An tsige Shugaban Majalisar Dokokin Kebbi

Majalisar Dokokin Jihar Kebbi ta tsige Shugabanta, Ismaila Abdulmumini Kamba da Mataimakinsa, Muhammadu Buhari Aliyu.

’Yan Majalisar sun tsige shugabannin nasu ne a zamansu na safiyar Talata ba tare da bayyana dalilinsu ba.

Mutum 20 cikin mambobin Majalisar ne suka amince suka kuma rattaba hannu don tsige shugabannin.

Sun kuma rantsar da dan Majalisa Muhammad Abubakar Lolo, mai wakiltar Bagudo ta Yamma a matsayin sabon Shugaban Majalisar, sai kuma Mohammaed Usman Zuru, mai wakiltar mazabar Zuru a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisa.