An tsige Shugaban Majalisar Dokokin Legas

Majalisar Dokokin Jihar Legas ta tsige shugabanta, Mudashiru Obasa, ta maye gurbinsa da Mojisola Meranda, mai wakiltar Mazabar Apapa I.

An tsige Shugaban Majalisar Dokokin Legas

Majalisar Dokokin Jihar Legas ta tsige shugabanta, Honorabul Mudashiru Obasa, daga kujerar shugabancin, inda ta maye gurbinsa da Honorabul Mojisola Meranda, mai wakiltar Mazabar Apapa I.

Majalisar ta kuma zabi Mataimakin Shugaban Mai Tsawatarwar, Fatai Mojeed, a matsayin mataimakin shugaban majalisar.

Takun sakar Obasa da majalisar ta fara ne tun bayan da kalaman da ya yi kan aniyar takarar zaben gwamna a shekarar 2027.

A watan Nuwambar 2024 lokacin da Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu yake gabatar da kasafin 2025 ne shugaban majalisar ya tayar da kura bayan da ya ce bai yi kankanta ba ko ya fito takara gwamna a 2027, yana mai cewa “wadanda suka rike kujerar ba fi na kwarewa suka yi ba.”

Ya kara da cewa, “Zan dauki gabarar tara mutane domin ganin hakan ya tabbata duk da kananan maganganun masu yi. Amma ina so in sanar cewa babban abin da na sa a gaba shi ne gina jam’iyyarmu ta kai dun inda ya kamata. Ni ba zama gwamna ne abin da ya fi min komai ba

Bayan nan ne aka zarge shi da kashe Naira biliyan 17 wajen gina kofar shiga harabar majalisar dokokin, baya ga zargin facaka da kudaden ayyukan mazabarsa.