An tsige Shugaban Majalisar Imo
Majalisar Dokokin Jihar Imo ta tsige Shugabanta, Chiji Collins saboda zargin almundahana. ’Yan Majalisar sun zabi Paul Emeziem daga Karamar Hukumar Onuimo a matsayin sabon Shugabansu. Hadimin Ganduje ya gwangwaje matasa da tallafin Jakuna Shugaban karamar hukuma ya yi wa mai neman kujerarsa dukan kawo-wuka Mutum 19 daga cikin ’yan Majalisa 27 ne suka tsige […]
Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma
Majalisar Dokokin Jihar Imo ta tsige Shugabanta, Chiji Collins saboda zargin almundahana.
’Yan Majalisar sun zabi Paul Emeziem daga Karamar Hukumar Onuimo a matsayin sabon Shugabansu.
- Hadimin Ganduje ya gwangwaje matasa da tallafin Jakuna
- Shugaban karamar hukuma ya yi wa mai neman kujerarsa dukan kawo-wuka
Mutum 19 daga cikin ’yan Majalisa 27 ne suka tsige Chiji Collins a zaman Majalisar na ranar Juma’a.
Sauran zarge-zargen da ya sa takwarorin Chiji Collins suka tsige shi sun hada da yin karfa-karfa da kuma saba ka’idojin aiki.