An tsige shugaban Majalisar Ogun
Elemide Oludaisi mai wakiltar mazabar Odeda ya zama sabon shugaban majalisar.
Majalisar Dokokin Jihar Ogun ta tsige shugabanta, Olakunle Oluomo.
A safiyar Talata mutum 18 daga cikin mambobin 26 da ke majalisar suka kada kuri’ar amincewa da tsige Oluomo mai wakilatar mazabar Ifo.
Kafin tsige Oluomo dai ana zargin sa da karkatar da kudaden majalisar Naira biliyan 2.5.
Bayan tsige shi mambobin majalisar suka zabi Honorabul Elemide Oludaisi mai wakiltar mazabar Odeda a matsayin sabon shugaban majalisar.
- Filato: An sa dokar hana fita na sa’a 24 a Mangu
- Hamas ta yi wa sojojin Isra’ila kisa mafi muni a rana guda a Gaza
Sabon shugaban majalisar, Elemide, ya mai goyon bayan tsohon gwamnan jihar Olusegun Osoba ne.
A baya ya janye daga takarar shugabancin majalisar ne domin ba wa Oluomo damar samun tazarce.