An tsige Shugabar Brazil
Majalisar Dattawan Kasar Brazil ta tsige Shugabar Kasar Dilma Rousseff bayan samunta da laifin yin amfani da kasafin kudin kasar don cimma bukatun kashin kanta. Matakin ya kawo karshen mulkin jam’iyya Workers’ Party wadda ta shafe shekara 13 tana mulki. Sai dai ta musanta duka zargin da ake mata. A yammacin yau Laraba ne ’yan […]

Majalisar Dattawan Kasar Brazil ta tsige Shugabar Kasar Dilma Rousseff bayan samunta da laifin yin amfani da kasafin kudin kasar don cimma bukatun kashin kanta.
Matakin ya kawo karshen mulkin jam’iyya Workers’ Party wadda ta shafe shekara 13 tana mulki. Sai dai ta musanta duka zargin da ake mata.
A yammacin yau Laraba ne ’yan Majalisa 61 suka kada kuri’ar tsige ta, yayin da guda 20 suka kada ta rashin amincewa da matakin.