An tsinci gawa a rataye cikin makarantar Islamiyya a Jigawa

An tsinci gawar wani mutum ɗan shekara 40 a cikin ajin wata makarantar Islamiyya a Karamar Hukumar Kiyawa a Jihar Jigawa.

An tsinci gawa a rataye cikin makarantar Islamiyya a Jigawa

Gawa

An tsinci gawar wani mutum ɗan shekara 40, Jibrin Adamu, a cikin ajin wata makarantar Islamiyya a Karamar Hukumar Kiyawa a Jihar Jigawa.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam, ya ce ’yan sanda sun gano gawar a rataye a saman silin din makarantar Miftahul Khairat Islamiyya da ke unguwar Gurdiba.

A cewar sa, jami’in ’yan sandan shiyya na Kiyawa da tawagarsa ne suka gano gawar a lokacin da suka isa wurin bayan sun samu rahoton.

DSP Lawan Shiisu Adam ya ce rundunar ’yan sandan ta kaddamar da bincike kan lamarin da ya faru a ranar Talata, 19 ga Satumba, 2024.

Ya kara da cewa marigayin, yana da tarihin matsalar tabin hankali kuma a wasu lokuta yana barin gida na tsawon kwanaki.

Ya ce a ranar mutuwarsa an ga Adamu yana dibar ruwa a kusa da makarantar inda daga bisani aka tsinci kansa a rataye a saman rufin.

Ya ce an kai gawar babban asibitin Dutse, inda aka tabbatar da mutuwar, kuma daga baya aka mika gawar ga ’yan uwansa domin yi masa jana’iza.

Shiisu ya bayyana cewa rundunar ’yan sandan jihar Jigawa tana kira ga duk wanda yake da labarin rasuwar Adamu da ya taimaka mata.

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato