An tsinci gawar ƙaramin yaro a ƙarƙashin gada

An tsinci gawar wani yaro ɗan kimanin shekaru uku da haihuwa a ƙarƙashin Gadar Oyun da hanyar zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilori a Jihar Kwara.

An tsinci gawar ƙaramin yaro a ƙarƙashin gada

Gawa

An tsinci gawar wani yaro ɗan kimanin shekaru uku da haihuwa a ƙarƙashin Gadar Oyun da hanyar zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilori a Jihar Kwara.

Aminiya ta gano cewa an tsinci gawar jaririn ne bayan ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka yi ranar Alhamis.

Kwamishinar Muhalli ta jihar, Nafisat Musa Buge, ta tabbatar wa wakilinmu faruwar lamarin.

Ta ƙara da cewa, “gawar ba za ta fi shekara uku da haihuwa ba. Kuma a yadda muka gan ta, da alama ruwan ambaliya ne ya kawo ta ƙarƙashin gadar.

“Na umarci ma’aikatan ma’aikatar cewa su jira, sai da aka jira tsawon awa 48 bayan tsintar gawar kafin a binne ta.”

Ta ce dalili shi ne, “Kwanaki mun binne gawar wata mata, amma washegari iyalanta suka zo cewa suna neman a tono gawar.”

Kwamishinar ta buƙaci iyaye su riƙa lura tare da sanin inda ’ya’yansu suke, musamman idan ana ruwan sama.

Ɗan sanda ya harbe kansa har lahira a Nasarawa

’Yan sanda sun kama baƙin haure 165 a Kebbi

Gobara ta yi ajalin almajirai 17 a Zamfara

Saura ƙiris Bello Turji ya zo hannu – Ministan Tsaro