An tsinci gawar Ɗan Majalisar da aka yi garkuwa a jajibirin Kirsimeti
An gano gawar Azuka da aka sace a jajibirin Kirsimeti a shekarar 2024 a kan gadar 2nd Niger Bridge, a cikin Anambra, ranar Alhamis.
![An tsinci gawar Ɗan Majalisar da aka yi garkuwa a jajibirin Kirsimeti An tsinci gawar Ɗan Majalisar da aka yi garkuwa a jajibirin Kirsimeti](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2025/02/Azuka.jpg)
An tsinci gawar mai shari’a Azuka, Ɗan Majalisa mai wakiltar mazaɓar Onitsha ta Arewa a Majalisar Dokokin Jihar Anambra.
An gano gawar Azuka da aka sace a jajibirin Kirsimeti a shekarar 2024 a kan gadar 2nd Niger Bridge, a cikin Anambra, ranar Alhamis.
- Uwa ta fusata ta jefa ’yarta cikin kogi a Bayelsa
- Yadda matar aure ta kashe dan kishiyarta da tafasasshen ruwa
Marigayin yana hanyarsa ta zuwa bukukuwan ƙarshen shekara ne tare da ‘yan uwansa a lokacin da ’yan bindiga suka yi awon gaba da shi a Ugwunakpamkpa da ke cikin garin Onitsha.
Sai dai jami’an tsaro da ke binciken sace shi sun cafke wasu da ake zargin sun kai su inda aka gano gawarwakin mambobin jam’iyyar Leba.
Da aka tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na ’yan sanda a Anambra, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin.
“Jami’anmu sun gano gawar yanzu. Kuma ina ganin ya kamata su kasance a kan hanyarsu a yanzu su kawo gawar nan (hedkwatar ’yan sandan jihar, Amawbia). Za mu sanar da manema labarai da zarar gawar ta iso nan,” in ji SP Ikenga
Da aka tambaye shi ya ba da cikakken bayani kan yadda aka gano gawar, sai ya ce, “Ina son Kwamishanan ‘yan sanda ya yi magana a kai. Ku jira kawai, zai yi wa manema labarai bayani a kai.”
Azuka shi ne ɗan majalisa a karo na biyu da aka kashe a Anambra a cikin shekaru biyu da suka gabata.