An tsinci gawar ɗan sandan da aka sace a Filato
An tsinci gawar ɗan sandan kwanaki bayan sace shi a yankin Wase.
An tsinci gawar wani jami’in ɗan sanda da aka sace a yankin Kampani da ke gundumar Bashar a ƙaramar hukumar Wase a Jihar Filato.
Idan ba a manta ba Aminiya, ta ruwaito yadda ’yan bindiga suka farmaki shingen tsaron tsaro a iyakar Jihar Taraba, inda suka farmaki wani soja da ɗan sanda.
- Shugaban Jam’iyyar APC na Oya ya mutu a Amurka
- Tinubu ya bayar da umarnin biyan tallafin man fetur – Rahoto
Sojan ya samu nasarar tsira, amma maharan sun yi awon gaba da ɗan sandan.
Wasu majiyoyi daga garin Wase sun tabbatar da cewa an samu gawar ɗan sandan a cikin daji a ranar Lahadi.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, bai ce uffan zuwa lokacin haɗa wannan rahoto ba.
Aminiya ta kuma ruwaito yadda a ‘yan kwanakin nan, mahara suka kai hari wasu yankuna na ƙaramar hukumar Wase a jihar.
A ranar 21 ga watan Mayu, 2024, Aminiya ta ruwaito yadda ’yan bindiga suka kai hari yankin Zurak, inda suka kashe sama da mutum 40, tare da raunata da dama, ciki har da ’yan banga da ke taimaka wa jami’an tsaro a yankin.