An tsinci gawar budurwa da aka aske wa gira a Kafanchan

A ranar Larabar da ta gabata ce aka tsinci gawar wata budurwa mai kimanin shekara 21 mai suna Deborah Stephen, bayan an tsige gashin idonta na gefe daya a kusa da Kotun daukaka kara ta Al’adu (Customary Court of Appeal) da ke kusa da ofishin Hukumar Tattara Haraji na garin Kafanchan da ke karamar Hukumar […]

An tsinci gawar budurwa da aka aske wa gira a Kafanchan
An tsinci gawar budurwa da aka aske wa gira a Kafanchan

A ranar Larabar da ta gabata ce aka tsinci gawar wata budurwa mai kimanin shekara 21 mai suna Deborah Stephen, bayan an tsige gashin idonta na gefe daya a kusa da Kotun daukaka kara ta Al’adu (Customary Court of Appeal) da ke kusa da ofishin Hukumar Tattara Haraji na garin Kafanchan da ke karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna.

Yayin da yake yi wa Aminiya bayani, daya daga cikin dangin yarinyar da ya bukaci a sakaye sunansa ya ce yarinyar ta bar gida ne da dare bayan ta amsa kiran waya daga wani wanda ba su tantance ko wane ne ba, inda tun daga lokacin ba ta dawo ba.

“Sai washegari da safe muka ji kira daga ofishin ’yan sanda cewa ana nemanmu a Babban Asibitin Kafanchan don duba wata gawa, kawai sai muka ga ’yarmu ce,” inji shi.

Ayarin Shugaban karamar Hukumar Jama’a, Honorabul danjuma Peter Aberik tare da na jami’an tsaro sun ziyarci gidan iyayen marigayiyar da ke Unguwar Masara a Gundumar Maigizo, karkashin masarautar Fantswam da ke bayan garin Kafanchan don halartar jana’izar yarinyar da aka gudanar da misalin karfe biyar na yammacin Laraba. Kuma bayan jajantawa shugaban ya kuma tallafa wa iyalan da abin yin jana’iza. 

Wadansu daga cikin wadanda Aminiya ta zanta da su wadanda suka ga gawar kafin dauke ta daga inda ake zargin an kashe ta ko an jefar da ita, sun ce ba su ga wata alamar duka ba amma dai an yanke girar saman idonta na gefe daya.