An tsinci gawar yarinyar da aka yi wa fyade a makabarta

Jama’ar unguwar Kurmin Mashi a Kaduna sun wayi gari cikin alhini bayan da suka gano gawar wata yarinya mai shekara shida da ake zargin an yi wa fyade, aka jefar da gawarta a makabarta. A ranar Lahadi 10 ga watan Nuwamba ne aka gano gawar yarinyar, wacce bayan ta dawo daga makarantar Islamiyya mahaifiyarta ta […]

An tsinci gawar yarinyar da aka yi wa fyade a makabarta

Jama’ar unguwar Kurmin Mashi a Kaduna sun wayi gari cikin alhini bayan da suka gano gawar wata yarinya mai shekara shida da ake zargin an yi wa fyade, aka jefar da gawarta a makabarta.

A ranar Lahadi 10 ga watan Nuwamba ne aka gano gawar yarinyar, wacce bayan ta dawo daga makarantar Islamiyya mahaifiyarta ta neme ta ta rasa bayan da ta fita waje yin wasa da yara.

Nan take aka bazama neman ta, inda daga baya wani manomi ya gano gawarta an turbude da kasa a cikin makabarta.

Kakakin ’yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Zuwa lokacin da aka tuntube shi ya ce rundunar ba ta tabbatar musababbin rasuwar yarinyar ba, amma binciken asibiti zai ba da tabbacin dalilin rasuwarta.

“Bayan an kallama bincike, asibiti zai hannanta gawarta ga iyayenta”, inji shi.

Ana iya tunawa wata hudu da suka gabata an gano gawar wata yarinya da aka yi wa fyade a yashe a cikin wani masallaci a unguwar.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa