An tsinci gawar jariri a cikin kwali a Lafiya
A ranar Litinin da ta gabata ce al’ummar Sabon Fegi da ke Lafiya fadar Jihar Nasarawa suka wayigari suka ga wani abin mamaki da tautsayi lokacin da suka ga gawar wani jariri a cikin kwalin talabijin yashe a cikin magudanar ruwa kusa da hanyar Lafiya zuwa Shendam. Tun misalin karfe 8:00 na safe jama’a da […]

A ranar Litinin da ta gabata ce al’ummar Sabon Fegi da ke Lafiya fadar Jihar Nasarawa suka wayigari suka ga wani abin mamaki da tautsayi lokacin da suka ga gawar wani jariri a cikin kwalin talabijin yashe a cikin magudanar ruwa kusa da hanyar Lafiya zuwa Shendam.
Tun misalin karfe 8:00 na safe jama’a da dama ciki har da masu abin hawa da suka fara tururwa don gane wa idonsu wannan abin tautsayi da mamaki.
Wani mai suna Malam Inusa Sabo da ke facin taya a kusa da inda aka jefar da jaririn ya shaida wa wakilinmu cewa “Da mitsalin karfe 6: 30 na safiyar Litinin na fito wurin aikina ina shara sai na ji kamar wani abu na motsi a cikin magudanar ruwa da ta wuce ta shagona. Da na leka ciki ne sai na ga wani kwalin talabiji na motsi. Nan take na dauka cewa miciji ne. Daga nan sai na kira wani mutum da ke tafiya a kan hanyar na gaya masa cewa ga wani abu fa yana motsi a cikin wani kwali a magudanar ruwan nan ina tunanin maciji ne. Da jin haka sai mutumin ya ce to bari ya nemo sanda ya bude kwalin don ya ga ko mene ne a ciki. Da ya bude kwalin ne sai muka ga jariri a ciki yana ta motsi.”
Ya kara da cewa “Da na tambaye shi abin da ya dace mu yi game da lamarin sai ya ce bari ya je Asibitin kwararru na dalhatu Araf ya sanar da su da yake asibitin yana kusa da wurin. Sai na ce shi ke nan ya yi sauri. Sai dai kafin ya zo da wani daga asibitin sai na ji yaron ya daina motsi. Da mutumin ya dawo da likita daga asibitin sai muka bayyana masa yadda lamarin ya auku. Da muka sake leka kwalin sai muka lura cewa jaririn ya mutu. Bayan likitan ya tabbatar da mutuwarsa sai ya shawarce mu cewa mu sanar da ’yan sanda lamarin ya koma.”
Ya ce daga nan ya sanar da ’yan sanda da ke kusa da su sai suka zo suka dauki jaririn.
Ya ce yana zargin karuwa ko wadda ta haihu ta haramtacciyar hanya ce ta jefar da jaririn a magudanar ruwa don wasu dalilai da ta sani.
Daga nan sai ya yi Allah wadai da wannan aikin keta da mahaifiyar jaririn ta yi, kuma ya shawarci mata su guji aikata irin wannan abu.
A nasa bangaren kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Conelius Ocholi ya tabbatar wa wakilinmu aukuwar lamarin inda ya ce gawar jaririn yana wurinsu kuma tuni rundunar ta soma bincike don gano matar da ta aikata wannan abu.
Ya ce idan aka kama matar za a tuhume ta kan zargin kisan kai. Ya shawarci ’yan mata su nemi sana’a da za ta taimaki rayuwarsu maimakon su rika bin maza suna rudinsu a karshe su zo suna da- na- sani.