An tsinci gawar kwamandan hukumar NDLEA a otel a Kalaba
An tsinci gawar Igbonna Uzoma, kwamandan hukumar da ke yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) a otel a Jihar Kuros Riba, a ranar Juma’a.
An tsinci gawar Kwamandan Hukumar Yaƙi da Ta’ammali da Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) na Jihar Kuros Riba, Igonna a wani otel da ke birnin Kalaba, a ranar Juma’a.
Rahotanni sun ce Uzoma, wanda aka dawo da shi aiki daga wata jiha zuwa Kuros Riba a kwanan nan, bai daɗe da kama aiki a sabon ofishin ba kafin wannan lamarin da ya jefa hukumar cikin ɗimuwa.
Kakakin NDLEA na ƙasa, Femi Babafemi, ya tabbatar da mutuwar babban jami’in, inda ya bayyana cewa an tsinci gawarsa a ɗakin otel ɗinsa a ranar Alhamis da ta gabata.
A cewarsa, “Kwamandan Ogbonna mutum ne mai tsananin jajircewa a aiki. An shirya fita aikin haɗin gwiwa tare da shi da misalin ƙarfe 10 na safiyar Alhamis, amma hakan bai samu ba. An kira wayoyinsa akai-akai babu amsa, har lokaci ya ƙure bai bayyana ba.”
- Takari: Rayuwar baƙin haure ’yan Najeriya mazauna Saudiyya
- Wata mata ta ƙone fuskar ’yar mijinta da tafasasshen man girki a Borno
Babafemi ya ƙara da cewa, “Duk da ƙoƙarin da ma’aikatan otel ɗin suka yi na buɗe ƙofar ɗakinsa, daga ƙarshe sai da aka yi amfani da makulli na musamman kafin a tarar da shi kwance ba shi da rai.”
Ya ce hukumar ta sanar da rundunar ’yan sanda ta jihar Kuros Riba nan take, inda kwamishinan ’yan sanda ya kai ziyara da kansa zuwa otel ɗin.
Yanzu haka bincike na ci gaba a kan asalin sanadin mutuwar kwamandan.
Shugaban hukumar NDLEA na ƙasa, Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya), ya bayar da umarni ga kwamandan shiyyar 14 na hukumar, ACGN Mathew Ewah, da ya gaggauta komawa Kuros Riba domin ɗaukar ragamar shugabancin hukumar a jihar, har sai an kammala binciken da kuma gano musabbabin mutuwar babban jami’in.