An tsinci gawar lauyar da ta bace a ofishinta

Yan sanda sun fara binciken zargin kashe wata lauya mai suna Misis Ijeoma Micah wadda aka iske gawarta a ofishinta da ke yankin Maitama, Abuja. Ijeoma, wadda ta mallaki kamfanin lauyoyi na Micah and Micah Chambers, an iske ta a mace ne bayan yini uku da bayyana bacewarta.Mijinta wanda aka ce ya zo Najeriya daga […]

An tsinci gawar lauyar da ta bace a ofishinta

Mohammed D. Abubakar Sufeto Janar na ‘Yan sandan NajeriyaYan sanda sun fara binciken zargin kashe wata lauya mai suna Misis Ijeoma Micah wadda aka iske gawarta a ofishinta da ke yankin Maitama, Abuja.
Ijeoma, wadda ta mallaki kamfanin lauyoyi na Micah and Micah Chambers, an iske ta a mace ne bayan yini uku da bayyana bacewarta.
Mijinta wanda aka ce ya zo Najeriya daga Landan a ranar Lahadin da ta gabata kuma ya garzaya ofishinta bayan da aka ce ya yi yini uku bai yi magana da ita ba ne ya yi kicibis da gawarta. Kuma nan take ya sanar da ofishin ’yan sanda na yankin Maitama.
Kwamishinan ’Yan sandan Abuja, Femi Ogunbayode ya ce daga binciken da suka fara, sun gano wasu mutane sun kira Ijeoma zuwa ofishinta domin wata hulda, inda ta tafi kuma daga nan ba a sake ji daga gare ta ba.
Ogunbayode ya ce sakamakon kisan, an kama jami’in tsaron da ke aiki da Ijeoma inda aka yi masa tambayoyi kan zargin hadin bakinsa.
Ya ce tunda jami’in tsaron bai kai rahoton batun ga ’yan sanda ba har mijinta ya dawo daga waje ya gano gawarta, don haka shi ma abin zargi ne.
Ya ce tuni masu binciken kwakwaf daga rundunar suka je ofishin da ake zargin an kashe matar, kuma tuni sun fara binciken lamarin.
Mutane a yankin sun ce mijin Ijeoma ya karya kofar ofishinta, kuma yana ganin gawarta ya shiga rusa kuka kamar zai kashe kansa. Kuma rahotanni sun ce ba a motar Ijeoma a gaban ofishinta inda ta saba ajiye ta a harabar ginin ba.