An tsinci gawar ma’aikacin gwamnati wata daya bayan sace shi
An samu gawar ma’aikacin a wani rami, wata daya bayan sace shi.
An tsinci gawar ma’aikacin Karamar Hukumar Katsina-Ala da ke Jihar Binuwai, a wani rami wata daya bayan an sace shi.
An gano gawar mutumin ne a wani rami a Akpera da ke yankin Tongov, a karamar hukumar.
- Ba zan daina fim saboda aure ba —Rahama Sadau
- Magidanci na neman diyya kan mutuwar matarsa yana tsare
- Wadanda suka kitsa harin Binuwe ba za su gujewa shari’a ba-Buhari
Rahotanni sun ce an sace mutumin ne wata daya da ya wuce, kuma iyalansa sun kasa gano inda yake.
Bayan gano gawar tasa, dan majalisar yankin da jami’an tsaro sun tona gawar tasa da aka binne.
Bayan tono gawar Myaan, an kai ta dakin ajiye gawarwaki na Babban Asibitin Katsina-Ala.
Da yake jawabi ga menama labarai, Shugaban Karamar Hukumar, Alfred Atera, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Yayin da wakilinmu ya yi kokarin ganawa da kakakin ’yan sandan jihar, DSP Catherine Anene, abun ya ci tura.