An tsinci gawar magidanci a rijiya a Kano

Hukumar Kashe Gobara ta Kano ta ciro gawar wani mutum mai shekaru kimanin 45 a cikin rijiya a garin Babawa da ke ƙaramar hukumar Gezawa. Kakakin rundunar, Saminu Yusuf Abdullahi ya ce wani dan sanda mai suna ASP Kabiru Abdullahi Lawan ne ya kira lambar gaggawa ta hukumar ya sanar da su lamarin. ’Yan fashi […]

An tsinci gawar magidanci a rijiya a Kano

Rijiyar Bajimba: Wadda ake dibar ruwa daga karfe 12 na dare zuwa 6 na safe Hoto daga Magaji Isah

Hukumar Kashe Gobara ta Kano ta ciro gawar wani mutum mai shekaru kimanin 45 a cikin rijiya a garin Babawa da ke ƙaramar hukumar Gezawa.

Kakakin rundunar, Saminu Yusuf Abdullahi ya ce wani dan sanda mai suna ASP Kabiru Abdullahi Lawan ne ya kira lambar gaggawa ta hukumar ya sanar da su lamarin.

“Sashin bayar da agajin gaggawa ne ya ciro gawar mutumin da karfe 1:25.

“Magidanci ne mai kimanin shekaru 45, sai dai ba a samu wanda ya san shi ko ya gane shi ba.

“Al’ummar unguwar sun ce sun gan shi ne a cikin rijiyar amma ba su san daga inda ya fito ba.

“Lokacin da aka fito da shi da ya rasu saboda dadewar da ya yi,” a cewar sanarwar.

Yanzu haka dai hukumar ta damƙa gawar ga ofishin ’yan sanda na Gezawa domin ci gaba da lalubo danginsa.