An tsinci gawar magidanci kwana biyu bayan ya fita amsa waya daga gida

Al’ummar Unguwar Ruga da ke garin Kubwa-Abuja sun samu kansu a cikin juyayi bayan tsintar gawar wani mazaunin yankin a jeji, kwana biyu bayan ya fita daga gidansa da dare. Matar marigayin mai suna Jamila ta shaida wa Aminiya a ranar Laraba da ta gabata cewa mijin nata mai suna Malam Umar Abubakar ya fita […]

An tsinci gawar magidanci kwana biyu bayan ya fita amsa waya daga gida

Al’ummar Unguwar Ruga da ke garin Kubwa-Abuja sun samu kansu a cikin juyayi bayan tsintar gawar wani mazaunin yankin a jeji, kwana biyu bayan ya fita daga gidansa da dare.

Matar marigayin mai suna Jamila ta shaida wa Aminiya a ranar Laraba da ta gabata cewa mijin nata mai suna Malam Umar Abubakar ya fita daga gida ne bayan an yi masa waya cewa ana bukatarsa a ranar Lahadin da ta gabata, bayan ya dawo daga Sallar Magariba, kuma tun daga lokacin ba a sake jin duriyarsa ba.

Bayana sun ce marigayin wanda makiyayi ne dan shekara 27 da ke da da guda, an tsinci gawarsa ne a ranar Talata da ta gabata, a karkashin wani tsauni a cikin jeji, daura da babban titin Kubwa zuwa Zuba tare da alamar kuna irin na salansan mashin a sawunsa sai kuma jini da ke fitowa daga bakinsa a duk lokacin da aka motsar da kansa.

Mahaifin marigayin mai suna Malam Adamu Abubakar, ya shaida wa Aminiya cewa a iya saninsa dan nasa bai da wata rashin jituwa da kowa, sannan ya bar komai ga Allah, ba ya zargin wani da hannu a lamarini.

Tuni aka yi jana’izar marigayin tun a yammacin ranar ta Talata. Babban jami’in ’yan sanda na garin Kubwa CSP Ayobami Surajudeen, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce a lokacin da aka sanar da ofishinsa faruwar lamarin, sun shawarci dangin mamacin da su kai maganar zuwa babban ofishin ’yan sanda na Gwagwa, wadanda ya ce su ne ke da hurumi a kan yankin da lamarin ya faru.