An tsinci gawar Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda a Oyo

Za a gayyaci wasu mutane domin yi musu tambayoyi kan lamarin, ciki har da waɗanda suka fara ganin gawarsa.

An tsinci gawar Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda a Oyo

An gano gawar wani Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda (DCP), Gbolahan Olugbemi a gidansa da ke Ogbomosho a Jihar Oyo.

Babban jami’in ’yan sandan da ke aiki a Legas ya yi gamo da ajalinsa ne yayin da ya je gida hutun bukukuwan Easter.

Marigayi Olugbemi wanda ya sha yabo da jinjina sanadiyyar rawar da ya taka a lokacin zanga-zangar #EndSARS ya mutu a wani yanayi mai ban mamaki.

Lamarin dai ya jefa jami’an hukumar binciken manyan laifuka (FCID) cikin alhini nan take.

A lokacin da Aminiya ta ziyarci ofishin FCID da ke Legas, an ga jami’ai rukuni biyu da uku suna tattaunawa a kan lamarin.

Sai dai rundunar ‘yan sandan ta bakin mai magana da yawun hukumar ta FCID, ASP Aminat Mayegun, ta ce za su gudanar da bincike a kan mutuwarsa.

Ta ce tsohon mataimaki na musamman ga marigayi DIG Israel Ajao da marigayi CP Young Arebamen ba su kashe kansu ba kamar yadda ake ta yayatawa ba.

Wata majiyar ‘yan sanda a FCID ta ce za a gayyaci wasu mutane domin yi musu tambayoyi kan lamarin, ciki har da waɗanda suka fara ganin gawarsa.

“Za mu gudanar da wannan bincike ne domin sanin inda marigayin ya je kafin rasuwarsa, da wanda yake tare da shi a lokacin da ya shiga ɗakinsa, ciki har da wanda ke da wayoyin hannu guda biyu har zuwa lokacin mutuwarsa,” in ji majiyar.