An tsinci gawar matashiya an jefar da ita tube a Abuja
Marigayiyar ta kira ’yan gidan cewa ga ta nan dawowa ta dauki cajar wayarta, daga nan ba su kara jin duriyarta ba har washegari
An tsinci gawar wata matashiya mai shekara 29 da aka jefar da ita a tube a cikin tafki a yankin Jikwoyi da ke Abuja.
A ranar Alhamis ne aka tsinci gawar matashiyar mai suna Blessing Moshood, wadda ta kammala karatu a Jami’ar Jihar Kogi da digiri mai darajar 2-1.
’Yar uwar margiyiyar mai suna Abigail, ta shaida wa wakilinmu cewa da farko Blessing ta bar gida da misalin karfe 8 na dare bayan ta gama waya.
Ba a jima ba marigayiyar ta kira ’yan gidan cewa ga ta nan dawowa ta dauki cajar wayarta, daga nan ba su kara jin duriyarta ba har washegari, lamarin da ya jefa mutanen gidan cikin damuwa.
Ta ce gada bisani suka samu labarin cewa “An tsinci gawar wata mace an jefar a cikin tafki, kuma kwatancen kitson wadda ake magana ya yi daidai da irin na ’yar uwata.
“Daga nan mahaifiyarmu ta fara kuka, daga bayan wasu ’yan sandan a caji ofis na Jikwoyi cewa an tsinci gawar a tube, babu riga a jikinta, an kai ta mutuwari a Mararraba da ke Jihar Nasarawa.”
Abigail ta ce da suka je caji-ofis na Jikwoyi ne aka nuna musu hoton gawar Blessing.
Wata makwabciyarsu mai suna Margaret ta bayyana marigayiyar a matsayin mutum mai basira da kuma faram-faram da jama’a.
“Ta kammala karatun jami’a da digiri ma darajar 2-1 a fannin Sociology,” in ji Margaret.
Wani makwabcinsu, Abdullahi Musa, ya roki ’yan sanda da su tsananta bincike da kuma fatattakar bata-garin da suka addabi yanin Jikwoyi.
Kakakin rundunar ’yan sanda ta Abuja, SP Josephine, ta tabbatar da faruwar lamarin tare da cewa rundunar tana gudanar da bincike a kan.