An tsinci gawar saurayi da budurwarsa a dakin otal

Wani matashi da budurwarsa sun gamu da ajalinsu bayan sun kwana a wani dakin otal a jihar Imo.  Saurayin mai suna Samuel Osoui da budurwarsa Cynthia Obieshi dalibai ne a Kwalejin Fasaha ta Gwamnatin Tarayya da ke Owerri a jihar Imo. Mai Magana da Yawun Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Imo, Orlando Okeokwu ya shaida wa […]

An tsinci gawar saurayi da budurwarsa a dakin otal

Wani matashi da budurwarsa sun gamu da ajalinsu bayan sun kwana a wani dakin otal a jihar Imo. 

Saurayin mai suna Samuel Osoui da budurwarsa Cynthia Obieshi dalibai ne a Kwalejin Fasaha ta Gwamnatin Tarayya da ke Owerri a jihar Imo.

Mai Magana da Yawun Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Imo, Orlando Okeokwu ya shaida wa Aminiya cewa tuni aka kai gawarwakin daliban dakin ajiyar gawa.

Ya ce, “A ranar Lahadi 14 ga watan Mayu, 2020, wasu mazauna rukunin gidajen dalibai suka ankarar da ‘yan sandan da ke aiki a yankin game da lamarin.

“‘Yan sandan sun shiga dakin otal din a gidan baki na Vic-Mic da ke yankin JMJ a Oweri inda suka karya kofar dakin suka iske gawar saurayin da budurwarsa a bisa gado.

“Bayanai sun nuna cewa buduwar ta ziyarci saurayin nata ne a jajibirin ranar sannan suka tafi otal din suka kwana.

“Binciken farko ya nuna sun sha wata kwaya ce da ta yi sanadiyar mutuwarsu, amma ana ci gaba da bincike domin sanin ainihin abin da ya yi sanadiyar mutuwar tasu”, inji shi.