An tsinci gawar tsohon dan kwallon Super Eagles a gidansa

Wani abin al’ajabi ya faru a ranar :Lahadin da ta gabata a garin Enugu bayan an tsinci gawar tsohon dan kwallon Najeriya Super Eagles mai suna Romanus Orjinta kamar yadda kafar sadarwar wasanni ta AfircanFootball.com ta kalato. Shi dai Orjinta dan kimanin shekara 33 da haihuwa ya taba yin wasa a kungiyar kwallon kafa ta […]

An tsinci gawar tsohon dan kwallon Super Eagles a gidansa

Wani abin al’ajabi ya faru a ranar :Lahadin da ta gabata a garin Enugu bayan an tsinci gawar tsohon dan kwallon Najeriya Super Eagles mai suna Romanus Orjinta kamar yadda kafar sadarwar wasanni ta AfircanFootball.com ta kalato.

Shi dai Orjinta dan kimanin shekara 33 da haihuwa ya taba yin wasa a kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles a tsakanin shekarar 2003 zuwa 2004 a karkashin horarwar Christian Chukwu. Kafin ya bar kungiyar sai da ya buga mata wasa har sau 13. Kwanaki kadan kafin rasuwar aka ji ya koka a kan yana fama da matsananciyar rashin lafiya.
Makwabta sun fara shiga damuwa ne saboda rashin jin duriyarsa na kwana biyu al’amarin da ya sa aka balle kofar gidansa kuma aka tsinci gawarsa a yashe da ya nuna ya kwana biyu da rasuwa.
Tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Christian Chkuwu ya kadu matuka da ya samu labarin rasuwar dan kwallon. Ya ce “a gaskiya na kadu da jin labarin rasuwar Orjinta don ban dade da rabuwa da shi a lokacin da aka gudanar da wata gasar cin kofi na matasan ’yan kwallo a garin Enugu ba.”
Ya ce ba zai manta irin zamna da suka yi da marigayin a kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ba a shekarar 2003 zuwa 2004 kuma dan kwallo ne mai kwazo da hazaka.
Marigayi Romanus Orjinta ba shi da mata ko ’ya’ya kuma yana zaune a gidansa ne a garin Enugu shi kadai.