An tsinci gawar wani mutum a kan titi a Kano

Ana zargin ‘yan daba ne suka shaƙe wuyan mutumin da waya.

An tsinci gawar wani mutum a kan titi a Kano

An tsinci gawar wani mutum da ba a san kowane ne ba yashe a kan titi a birnin Kano.

An tsinci mutumin a kan titin zuwa gidan gwamnatin jihar a ranar Litinin.

A cewar wasu mutane da ke kusa da wajen da aka tsince gawar, suna zargin wasu bata-gari ne suka makure wuyansa da wayar lantarki har sai dai suka tabbatar ya daina numfashi.

Sai dai an garzaya da shi zuwa Asibitin Koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase domin ba shi agajin gaggawa.

Kokarin da wakilinmu ya yi domin jin ta bakin kakakin ‘yan sandan jihar, SP Haruna Abdullahi Kiyawa, ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Suka Sa Farashin Citta Ta Yi Tashin Gwauron Zabo

Wike ya ƙwace filayen jiga-jigan ’yan siyasa a Abuja

Gwamnoni sun ƙi amincewa da ƙara harajin VAT

Matashi ya kashe mahaifinsa kan N5,000 a Delta