An tsinci gawar wani tsoho a otal a Jigawa

Rundunar ta ce tana ci gaba da bincike domin gano musababbin rasuwar mtumin.

An tsinci gawar wani tsoho a otal a Jigawa

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, ta fara bincike kan mutuwar wani mutum mai shekaru 60 da ya rasu bayan ya kamu da rashin lafiya a wani otal da ke Dutse, babban birnin jihar.

’Yan sanda sun ce lamarin ya faru ne a ranar Talata da misalin ƙarfe 12:50 na rana.

Mutumin ya shiga otal ɗin tare da wata budurwa mai shekaru 20, kuma bayan ya ba da umarnin a kawo masa abinci ne, ya fara samum matsalar numfashi.

Jami’an Sashen ’Yan Sandan Yalwawa, sun isa wajen bayan samun kiran gaggawa, sannan suka garzaya da shi zuwa Babban Asibitin Dutse, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.

’Yan sanda sun samo abinci, abubuwan sha da maganin ƙara ƙarfin maza tare da wasu kayayyakin marigayin a ɗakin otal ɗin.

An ajiye kayayyakin domin gudanar da binciken kimiyya a kansu.

Bayan kammala nazari da matakan da suka dace, an miƙa wa iyalan mamacin gawarsa domin yi masa jana’iza.

Rundunar ta kuma ce budurwar mai shekaru 20 da ke tare da marigayin tana bayar da haɗin kai wajen bincike da bayanan da za su taimaka wajen gano abin da ya faru.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Jigawa, ya tabbatar wa al’umma cewa za a gudanar da binciken cikin adalci da ƙwarewa.

Ya kuma buƙaci jama’a da su guji yaɗa jita-jita ko bayanan da ba a tabbatar da su ba yayin da ake ci gaba da bincike.

’Yan sanda sun ce za yi ƙarin bayani idan sun kammala bincike.

Uba da ’ya sun mutu a rijiya a Kano

An tsinci gawar wani tsoho a otal a Jigawa

Zidane ya zama sabon kociyan Faransa

An kama wani mutum da ƙunshi 28 na tabar wiwi a Katsina