An tsinci gawar wata ɗaliba a cikin ɗaki a Kano
Aisha, ɗaliba ce da ke shekara ta fannin nazarin Kimiyya da Fasahar Abinci na jami’ar.
An tsinci gawar wata ɗaliba mai suna Aisha Yahaya ta Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil, a wani gida da ke wajen jami’ar.
Aisha, ɗaliba ce da ke matakin karatu na uku wato level 300 a sashen nazarin Kimiyya da Fasahar Abinci na jami’ar wadda aka tsinci gawarta bayan ta koma ɗakinta.
An ce ɗalibar ta rubuta jarrabawarta ta farko a zangon karatun na farko da ake yi a jami’ar.
Wasu daga cikin abokan karatunta sun danganta mutuwarta da shiga cikin matsi da damuwa a dalilin karatu da kuma zana jarrabawar.
A cikin wasiƙar ta’aziyyar, hukumar jami’ar ta bayyana matuƙar baƙin cikinta dangane da rasuwar Aisha Yahaya.
Sanarwar ta ce, “Aisha ɗaliba ce mai hazaƙa wadda ta rasu a dalilin bugun zuciya. Za a riƙa tunawa da ita a kan sha’awarta na karatu da jajircewarta kan harkokin karatunta.”
Jami’ar ta ƙara da cewa, ba a iya gano wata da ke tattare da ita ba gabanin mutuwarta saboda ba ta nuna alamun rashin lafiya ko fama da wata cuta ba.