An tsinci gawar wata mace a gonarta
Al’ummar Tungan-Dallatu da ke karamar Hukumar Birni da Kewayen Abuja sun wayigari a ranar Talatar makon jiya cikin juyayin rashin wata yar yankin da aka kashe ta a gonarta ta hanyar shake ta tare da yi mata fyade. Mai unguwar yankin Malam Adamu danladi wanda suruki ne ga marigayiyar, ya ce matar mai suna Rakiya […]
Al’ummar Tungan-Dallatu da ke karamar Hukumar Birni da Kewayen Abuja sun wayigari a ranar Talatar makon jiya cikin juyayin rashin wata yar yankin da aka kashe ta a gonarta ta hanyar shake ta tare da yi mata fyade.
Mai unguwar yankin Malam Adamu danladi wanda suruki ne ga marigayiyar, ya ce matar mai suna Rakiya Ibrahim wanda mijinta ya rasu a shekarun baya, ta ziyarci gonarta inda ta shuka doya da misalin karfe 4:00 na yamma a ranar don gudanar da wasu ayyuka, amma sai aka ga ba ta dawo gida ba har bayan faduwar ranar wunin.
Ya ce bayan da aka gano ba ta dawo gida ba, wadansu daga cikin iyalansu sun bazama dajin da gonar take inda suka tarar da gawarta an daure mata wuya da fallen zanenta kuma an cika bakinta da idonta da kasa. Mai unguwar ya ce sun sanar da ’yan sandan Zuba faruwar lamarin sannan suka dauko gawar tare da ’yan sandan aka yi mata jana’iza washegari.
Ya ce a binciken da matan yankin suka gudanar a jikin marigayiyar wadda ta rasu ta bar ’ya’ya shida, sun gano cewa akwai yiwuwar makasanta sun yi mata fyade kafin ko bayan kashe ta.
Babban Jami’in ’Yan sandan Zuba (DPO), CSP Ayobami Surajudeen ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce suna gudanar da bincike a kai.