An tsinci gawar wata mata a kusa da Jami’ar Tarayya a Yobe

Rundunar ta jaddada ƙudirinta na ci gaba da kare rayukan al’umma a jihar.

An tsinci gawar wata mata a kusa da Jami’ar Tarayya a Yobe

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe, ta gano gawar wata mata mai suna Falmata Abubakar, mai kimanin shekaru 45, wadda aka kashe a kusa da Jami’ar Tarayya Gashuwa (FUGA), da ke Ƙaramar Hukumar Bade.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7 na safe a ranar 17 ga  watan Oktoba, 2025, bayan wani mazaunin unguwar Sabon Daula mai suna Yusuf Sarkin Baka, ya kai rahotn ganin gawar.

’Yan sanda sun isa wajen, inda suka tabbatar cewa mamaciyar ita ce Falmata Abubakar, mazauniyar Abasha, unguwar Sarkin Hausawa.

An same ta sanye da baƙin hijabi, kwance babu rai.

An kai gawar Asibitin Ƙwararru na Gashuwa, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarta.

Bayan kammala bincike, an miƙa iyalanta gawarta domin yi mata jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Rahotanni sun nuna cewa an jefar da gawar marigayiyar ne, kimanin kilomita biyu da gidanta.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Yobe, CP Emmanuel Ado, ya tabbatar da cewa rundunar ta fara bincike domin gano waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki.

Ya kuma roƙi jama’a su kwantar da hankalinsu, tare da bai wa ’yan sanda haɗin wajen bincike.

Rundunar ta jaddada ƙudirinta na kare rayuka, dukiyoyi da tabbatar da zaman lafiya a faɗin jihar.